Hukumar Bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta ce akwai hasashen jihohin ƙasar 31 da ƙananan hukumomi 148 ka iya fuskantar ambaliya a damunar bana.
Hukumar ta buƙaci gwamnatocin jihohin ƙasar da su bi gargaɗinta sannan su aiwatar da matakan kariya daga bala’in ambaliya domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi al’umma.
Shugabar hukumar, Zubaida Umar wadda ta tabbatar da hakan a yayin wata ganawa da jami’an gwamnatin jihar Edo, ta nanata muhimmancin haɗa ƙarfi da ƙarfe da jihar wajen samar da shirin ko-ta-kwana domin tunkarar barazanar ta ambaliya.
Hukumar ta NEMA dai ba ta lissafa jerin sunayen jihohin da ƙananan hukumomi ba amma ta ce yawanci birane da garuruwan da ke kusa da ruwa ka iya fuskantar barazanar.