Friday, December 26
Shadow

Gidajen Talakawa Milyan Biyar Ne Suka Amfana Da Tallafin Naira Bilyan 493 Da Shugaba Tinubu Ya Raba”>>Inji Gwammati

“Gidajen Talakawa Milyan Biyar Ne Suka Amfana Da Tallafin Naira Bilyqn 493 Da Shugaba Tinubu Ya Raba”.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya cire takunkumin da aka saka kan asusun Hukumar Shirin Zuba Jarin Jin Kai ta Ƙasa “National Social Investment Programme Agency (NSIPA)”, wanda ya kai ga sakin sama da Naira biliyan 493 domin tallafawa gidaje miliyan biyar a fadin ƙasar. Tun a ranar 8 ga Janairu, 2024 ne aka dakatar da Ministar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Dr Betta Edu, tare da umartar Hukumar Yaƙi da Laifukan Tattalin Arziki da Kuɗi (EFCC) ta gudanar da bincike kan duk wasu harkokin kuɗi na ma’aikatar da hukumomin da ke karkashinta. Haka kuma, Shugaban Ƙasa ya kafa kwamiti karkashin jagorancin Ministan Kudi, Wale Edun, domin duba tsarin kuɗi na shirin jin kai da inganta shi don amfanin talakawa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo Da Duminsa: Gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta iso Najeriya

Karamin Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Dr Yusuf Sununu, ya bayyana farin cikinsa game da wannan mataki a taron manema labarai, inda ya ce gwamnatin tarayya na da kasafin kuɗi sama da Naira biliyan 500 da aka ware don aiwatar da shirye-shiryen tallafi kamar Shirin Ciyar da Dalibai a Makarantu na Ƙasa (National Homegrown School Feeding Programme), Shirin Ba da Kuɗi ga Talakawa (Conditional Cash Transfer), Shirin Ƙarfafa Matasa da Horas da su na N-Power, da kuma Tallafin Kuɗi ga Manoma (FarmerMoni). Ya ce umarnin Shugaban Ƙasa ya ba da damar bude asusun NSIPA don fara aiwatar da Shirin Tallafawa Ƙananan Ƙungiyoyi da Ƙarfafa Harkokin Kasuwanci “Government Enterprises and Empowerment Programme (GEEP)” da kuma wasu shirye-shirye masu muhimmanci.

Karanta Wannan  Nan da shekarar 2074 Najeriya sai ta fi kasashen Saudiyya, Ingila, Canada da Japan karfin tattalin Arziki>>Inji Bankin Kasar Amurka

Dr Sununu ya kara da cewa, ana shirin kaddamar da Tallafin Kuɗi ga Ƙungiyoyin da ke Cikin Ƙalubale “Grant for Vulnerable Groups (GVG)” a nan gaba kadan. Ya ce ma’aikatar ta dauki kamfanoni 53 da za su taimaka wajen sabunta rajistar NIN ga wadanda ke cikin “National Register” da ba su da lambar asusun banki, Lambar Shaidar Ƙasa (NIN) ko Lambar Tantancewar Asusun Banki (BVN), domin su samu damar amfana da tallafin gwamnati cikin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *