
Jam’iyyar PDP, Reshen jihar Sokoto ta bayyana cewa, kamun da akawa tsohin Gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal siyasa ce.
Me magana da yawun jam’iyyar, Hassan Sanyinnawal ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai da safiyar ranar Talata.
Yace EFCC ta bar asalin masu rashawa da cin hanci inda take kama irin su Tambuwal. Yace hakan kokari ne na dakile ‘yan Adawa da kuma hana yiwa shugaba Tinubu suka da gaya mai gaskiya.
Ya yi kira ga masoyan Tambuwal su kwantar da hankali amma su tsaya kai da kafa wajan goyon bayansa.