
Matatar man fetur din Dangote ta sanar da rage farashin man fetur dinta da Naira 30..
Me kula da harkar sadarwa na matatar, Anthony Chiejina ne ya bayyana hakan inda yace ragin farashin zai fara aiki ne nan take.
Yanzu za’a rika sayen man fetur din akan naira 820 maimakon 850 da ake sayarwa a baua.
Matatar tace zata ci gaba da samar da wadataccen man a duka fadin Najeriya