
Gwamnatin kasar Amurka tace duk dan Najeriyar dake neman Visa ta shiga kasarta dolene ya nuna yanda yake amfani da kafafen sadarwa na tsawon shekaru 5 baya.
Dokar tace kin yin hakan zai iya sa a hana mutum Visar shiga kasar Amurkar.
Saidai cikin gaggawa, Gwamnatin taraya ta sha Alwashin daukar irin wannan mataki akan ‘yan kasar Amurka masu shigowa Najeriya.
Kasar Amurka ta bayyana wannan sabuwar dokane ta kafar X wanda tace hakan na daga cikin shirin shugaban kasarta, Donald Trump na ganin ya samarwa kasar tasa tsaro.
Me magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Najeriya, Kimiebi Ebienfa ya bayyana cewa, Gwamnatin kasar Amurka tuni ta sanar dasu wannan shiri.
Yace itama Najeriya zata dauki irin wannan mataki akan ‘yan kasar Amurka masu neman Visa a Najeriya.