
Hukumar hana yiwa tattalin arziki kasa zagon kasa, EFFC ta bayyana cewa, zata fara binciken tsohon shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari kan zargin satar Dala Biliyan $7.2 na gyaran matatun man Najeriya.
Hakan na zuwane bayan da tuni kotu ta kulle asusun ajiyarsa na banki guda 4 dake dauke da makudan kudade.
Rahoton Daily Trust yace tuni aka fara binciken wasu na kusa da Kyari inda EFCC tace tana son samun isassun bayanai akanshi kamin ta fara bincikenshi.
Game da cewa, Kyari baya Najeriya, Hukumar tace wannan ba matsala bane da zarar sun bukaci kamashi ko bincikenshi kamashi ba abune me wuya ba.