Thursday, November 26
Shadow

Da Duminsa: Kotu ta saurari karar da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya shigar da ICPC da DSS a yau inda yake neman Jimullar Naira Biliyan 3

Rahotanni sun bayyana cewa, babbar kotun tarayya dake Abuja ta saurari karar da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya shigar inda yake kalubalantar tsareshi da ake yi da kuma zarge-zargen da ake masa.

Me magana da yawun Malam Nasiru, Muyiwa Adekeye ne ya bayyana hakan inda yace a yau, Kotun na sauraren karar take hakkin malam da ya shigar.

Kotu taji duka bangarorin me kara da wanda ake kara inda ta daga karar zuwa ranar 27 ga watan February dan baiwa wanda ake karar damar tattara bayanai.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda fadawan sarkin Katsina suka fasa kofar taro suka shigar da sarkin bayan da aka kulle kofar dakin Taron da aka yiwa Tinubu Maraba a jihar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *