Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyon: Hotunan da aka rika yadawa ina daukar hoto, tsaffin hotunane>>Gwamna Dikko Radda

Gwamnan jihar Katsina, Umar Dikko Radda ya bayyana cewa, Hotunan da aka rika yadawa inda aka ganshi yana daukar hoto a kasashen Turawa tsaffin hotunane.

Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi.

!A lokacin da aka kai hari wani kauyen Mantau dake Malunfashi jihar Katsina inda aka kashe masallata da yawa, an rika yada hotunan inda aka rika cewa, Gwamna na can kasashen Turai yana hutawa yayin da aka kashe mutane a jihar Katsina.

Gwamna Dikko Radda yace neman lafiya yaje, kuma yace a wancan lokacin shi ba gwamnan jihar Katsina bane, sabida ya mika ragamar mulki a hannun mataimakinsa.

Karanta Wannan  Ko NLC na iya tilasta wa gwamnoni biyan albashi mafi ƙanƙanta?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *