
Jam’iyyar APC ta lashe ƙananan hukumomi 20 cikin 23 a zaɓen ƙananan hukumomi jihar Rivers da aka gudanar a jiya Asabar.
A ɗaya ɓangaren kuma, jam’iyyar PDP mai mulki a jihar, ta samu nasarar lashe ƙananan hukumomi uku, kamar yadda hukumar zaɓen jihar ta sanar.
Dakataccen gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya sha kaye a ƙaramar hukumarsa ta Opobo-Nkoro, inda ɗan takarar jam’iyyar APC ya lashe zaɓen.
Shugaban hukumar zaɓen, Dr Michael Odey ne ya sanar da sakamakon zaɓen a hedkwatar hukumar da ke titin Aba a Fatakwal kamar yadda jaridar Punch mai zaman kanta ta ruwaito.
A bara dai an yi wani zaɓen, inda Fubara ya tsayar da na hannun damarsa a jam’iyyar APP, inda suka doke ƴan takarar Wike a zaɓen, amma mutanen tsohon gwamnan suka je kotu, inda aka yi ta tafka shari’a har kotun ƙoli ta soke zaɓen daga baya.
Bayan sulhu tsakanin Fubara da Wike wanda Tinubu ya jagoranta aka shirya wannan zaɓen, inda tun farko aka ce an tsara yadda ake so ta kasance.