
Tauraron Tiktok, Gfresh Alamin ya bayyana cewa, yayi sabuwar amarya.
Ya bayyana hakane a shafinsa na Tiktok inda aka ganshi da sabuwar amaryar tasa suna nishadi.
Yace yana fatan sabuwar amaryar tasa zasu zauna lafiya da matarsa.
Saidai ba’a ga sanda aka daura aure ba, ko kuwa watakila a boye aka Daura auren?