Friday, December 26
Shadow

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayar da labarin irin cin amanar da aka masa a shekarar 2015 da ya nemi sake cin zabe a karo na 2

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayar da labarin yanda ta kaya a shekarar 2015 da ya nemi sake cin zabe a karo na biyu.

Ya bayyana hakane a yayin da ya je bikin cikar Chief Mike Aiyegbeni Oghiadomhe shekaru 50 da haihuwa.

Yace yawanci ‘yan siyasa sun yaudareshi ne a 2015, yace siyasar Najeriya akwai cin amana sosai a cikinta, yace da wuya ka samu wanda zai tsaya kan magana daya ta gaskiya.

Yace amma Chief Mike Aiyegbeni Oghiadomhe mutum ne me nagarta wanda yana sonshi da gaske.

Karanta Wannan  Na tsynèwà duk wani Tshàgyèràn Dhàjì na kasarnan kuma Najeriya ba zata taba zama kasar Musulmi ba>>Inji Fasto Oyedepo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *