
Tauraron fina-finan Hausa, Tahir Fage ya bayyana cewa, karfin hali yake fina-finan da yake fitowa saboda yana fama da ciwon zuciya
Yace ana neman sama da Naira Miliyan 2 dan a masa aiki a Abuja.
Ya bayyana hakane a hirar da RFIHausa Suka yi dashi.
Ya kuma ce Ko rawar gala da aka ga yayi a kwanakin baya yana neman dubu 250 ne yaran da suka bude gidan galar suka bashi Naira dubu 100 dan ya je a matsayin babban bako.