
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya baiwa al’ummar Jihar Hakuri inda yace kamin ya hau mulki yayi Alkawarin rika bayar da ba’asi kan yawan kudaden da aka samu da wanda aka kashe.
Yace amma bayan da ya hau yaga abin ba mai yiyuwa bane.
Gwamnan yace dalili kuwa shine Wasu kudaden idan aka karbosu kudin aikin gwamnatin data wucene za’a biya, hakanan wasu kudaden kuma aikin da aka yi shekarar data wucene za’a biya dasu.
A karshe dai yace shima dan Adam ne dan haka yana neman Afuwa.
Kalli Bidiyon jawabinsa a kasa;