Farashin Naira yayi kasa yayin da aka shiga hutun Sallah.
Rahoto ya bayyana cewa farashin Naira ranar Juma’a shine 1,482.72 akan kowace dala daya wanda idan aka kwatantashi da farashin Nairar na ranar Alhamis, watau 1,476.24, farashin yayi sama.
Wannan farashin gwamnati ne yayin da a farashin kasuwar bayan fage aka sayar da dalar akan Naira 1,490.