Friday, December 26
Shadow

Lauyoyin Nnamdi Kanu sun bayyana cewa, basu yadda da Sakamakon gwajin Lafiyar da aka masa ba inda suka ce ko jininsa ba’a dauka ba ta yaya za’a ce yana da lafiyar da zai iya ci gaba da tsayawa a gaban kotu?

Lauyoyin Nnamdi Kanu sun bayyana cewa, basu yadda da sakamakon gwajin Lafiyar da aka masa ba inda suka ce ta yaya gashi an tabbatar bashi da lafiya amma ace wai zai iya tsayawa a gaban Kotu.

Lauyoyin bayan zaman kotun a yau, Alhamis sun bayyana cewa, suna kira ga kungiyar Likitoci ta kasa data kiyaye kada ta batawa kanta suna.

A baya dai sakamakon da likitoci suka fitar akan Lafiyar Nnamdi Kanu sun ce zai iya ci gaba da tsayawa a gaban kotu dan ci gaba da masa shari’a sannan kuma Asibitin sha ka tafi na DSS zai iya ci gaba da dubashi saboda rashin lafiyar tasa bata yi tsanani ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda sojan Najeriya yayi bayanin Abashi da Alawus da suke dauka dalla-dalla

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *