
Wata matar aure Mulikat Yusuf ta yanke jiki ta fadi sumammiya bayan da mijinata ya saketa a kotu duk da kai kara da ta yi akan kada ya saketa.
Matar ta kai mijinta, Ishaq Abdulganiyu kara inda tacewa kotu ta haifa masa yara 6 kuma ita yanzu idan ya saketa bata san inda zata ba.
Saidai mijin yace babu ruwansa da ita.
A hanyarta ta fita daga kotun ta yanke jiki ta fadi.
Saida aka yayyafa mata ruwa ta farfado.
Lamarin ya farune a kotun dake Igboro, Ilorin jihar Kwara.
Alkalin kotun, Toyin Oluko ya baiwa matar shawara ta je ta lallaba mijinta.
An daga ci gaba da sauraren shari’ar har zuwa 5 ga watan Disamba, inda alkalin yace ya basu damar su shirya kamin lokacin ko kuma a ci gaba da shari’a.