
Gwamnan jihar Naija, Umar Bago ya baiwa mutanen jiharsa shawarar su tashi tsaye su kare kansu.
Yace matsalar garkuwa da mutane dan neman kudin fansa a jihar ya kai matakin yaki inda yace dole sai an tashi tsaye.
Gwamnan yace, ba zai biya kudin fansa ba kuma babu maganar sulhu da ‘yan Bindigar yace idan aka rika basu kudi, zasu mayar da abin kasuwanci.
Gwamna Bago yace kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa kowane dan kasa damar kare kansa da Dukiyarsa.