Friday, December 26
Shadow

Dalilin da ya sa na sauya hafsoshin tsaron Najeriya – Tinubu yayi karin bayani

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa ya ɗauki matakain sauya hafsohin tsaron ƙasar, yana mai gode wa tsofaffin manyan jami’an tsaron da ya sauke.

Wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ya ce ya ɗauki matakin ne saboda “ƙyautata tsaron ƙasa”

“Na amince da sauya shugabancin rundunar tsaro domin ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya,” in ji shi.

“Ina gode wa Janar Christopher Musa da sauran hafsoshin tsaron da suka gabata saboda hidima da sadaukarwar da suka yi, kuma ina neman sababbin shugabannin da su kyautata ƙwarewar aiki, da ankararwa, da haɗin kai a tsakanin sojojinmu.”

Sauyin shugabannin rundunar sojin na zuwa ne a lokaci da ake ci gaba da raɗe-raɗi game da shirin juyin mulki da aka ce wasu sojoji sun tsara, zargin da rundunar sojin ta musanta.

Karanta Wannan  Hajj 2025: Maniyyata fiye da 2000 sun tashi zuwa ƙasa mai tsarki

Sunayen sabbin hafsoshin tsaro:

  • Janar Olufemi Oluyede – Hafsan hafsoshi.
  • Manjo Janar W Sha’aibu – Hafsan sojojin ƙasa.
  • Air Vice Marshall S.K Aneke – Hafsan sojin sama.
  • Rear Admiral I. Abbas – Hafsan sojin ruwa.
  • Manjo Janar E.A.P Undiendeye – Shugaba sashen tattara bayan sirri na soji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *