
Wata Inyamura data bar Kiristanci zuwa Addinin Musulunci ta bayyana cewa bincikene ya kaita ga gane cewa Addinin Musulunci shine addinin Gaskiya.
Ta bayyana hakane a wani Bidiyo data wallafa ind aka ganta tana cewa, Data yi bincike akan Yahudanci ta gane cewa su basa son A shiga addinin su, wanda aka haifa a cikin Addinin shine kadai Bayahude na gaskiya.
Sannan tace a Kiristanci kuma akwai abubuwan rudarwa da yawa inda tace data yi bincike akan addinin musulunci ne ta samu nutsuwa ta kuma karbi Musulunci.