
Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu ya bayyana cewa Allah ya riga ya kaddarowa Atiku Abubakar cewa ba zai zama shugaban kasar Najeriya ba.
Yayi kira ga Atiku da ya hakura da kaddarar da Allah ya doro masa cewa ba zai zama shugaban Najeriya.
Atiku dai tin a shekarar 1992 yake neman takarar shugabancin Najeriya amma bai samu ba.
Ya bayyana hakane ga manema labarai a fadarsa yayin da yake bikin cika shekaru 22 da hawa karagar sarautar Birnin na Legas.
Yace shi kuma Tinubu zabin Allah ne dan haka yana kira ga ‘yan Najeriya da su goya masa baya.