
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa har yanzu yana kokarin ganawa da shugaban kasar Amirka, Donald Trump.
Ya bayyana hakane ta bakin me bashi shawara kan harkar sadarwa, Watau Daniel Bwala a hirar da aka yi dashi a Arise TV.
Daniel Bwala yace kwanannan Shugaba Tinubu da Donald Trump zasu gana dan karfafa dangantakar Najeriya da kasar ta Amurka.
Ya bayyana cewa ba zai bayyana irin shirin da suke ba amma mutane au fahimci cewa har yanzu suna kokarin ganin an bi hanyar data dace dan ganawa tsakanin shuwagabannin biyu.