
Rahotanni sun bayyana cewa, Rashin aikin yi a tsakanin matasan kasar Amurka yayi Qamari.
Rahoton wanda gidan jaridar Fortune ya wallafa yace a tsakanin matasa masu shekaru tsakanin 22 zuwa 27, rashin aikin yin su iri daya ne, babu banbanci tsakanin wanda yaje makaranta da wanda bai kammala Digiri ba.
Rahoton yace rashin aikin yi a tsakanin matasan ya kai makin kaso 5.5 cikin 100.
Rahoton yace kamfanoni da yawa da masu daukar aiki sun rage baiwa kwalin Digiri muhimmanci.
Hakan yasa matasa suka fara barin karatun Digiri suna komawa makarantun koyon sana’a.