
Hukumar kula da jami’o’in Najeriya NUC ta gargadi masu Digirin girmamawa ta Doctorate da cewa su daina amfani da “Dr.” A gaban sunansu.
Hukumar tace wadanda suka yi karatun PhD ne kadai ke da ikon amfani da “Dr.” A gaban sunansu.
Shugaban hukumar ta NUC, Prof. Abdullahi Ribadu ne ya bayyana haka a wajan kaddamar da wani bincike da aka gudanar akan bayar da Digirin Doctorate na girmamawa da jami’o’i ke yi.
Ya bayyana cewa akwai damuwa kan yanda ake amfani da Digirin Doctorate na girmamawa ta hanyar da bata kamata ba