
‘Yan Bìndìgà da suka yi garkuwa da daliban makarantar MAGA dake jihar Kebbi sun bugi Qirji cewa Gwamnati ta kasa karbar dalibai ta Qarfi sai Sulhu aka yi suka bayar da daliban.
A Bidiyon da suka saki, an jisu suna tambayar daliban shin Jiragen sama nawa suka ji sun wuce ta saman su suka ce basu san iyaka ba.
Sannan sun tambayi daliban cewa, ko an tabasu ko an ci zarafinsu? Suka ce a’a.