
Malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa, yafi damuwa da Tshàgyèràn Dhàjì fiye da mutanen da suke yin Garkuwa da su.
Malam ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace kamar a Asibiti ne idan aka kawo mutum na zubar da jini, ana fara tsayar da jinin ne farko kamin a fara gyaran ciwo ko dinki.
Malam yace misali Mahaukaci ne a kasuwa ya cakawa mutane da yawa wuka, kamata yayi a fara kwace wukar dake hannunsa kamin a fara kula wadanda ya cakawa wukar.
Yace bawai bai damu da wadanda lamarin ‘yan Bindigar ke shafa ba, abinda yake magana akai shine a fara dakatar da zubar da jinin tukunna.