A ranar Talatar nan ne mahajjata miliyan ɗaya da 800,000 suke ƙarƙare aikin Hajjin bana, bayan kammala jifan shaiɗan kamar yadda aka fi sani.
Ana dai yin jifan ne a ranakun 10 da 11 da 12 inda mahajjatan ke tsintar ƙananan duwatsu guda bakwai a kowane domin jifan kowacce Jamrat daga jamrori uku.
Sai dai wasu mahajjatan kan zaɓi ƙara kwana ɗaya kamar yadda addinin Musulunci ya ba su dama, inda sai zuwa ranar Laraba ne za su bar Mina zuwa Makka.
Yayin da wasu alhazan sai sun koma Makka ne za su yi ɗawafi da sa’ayi, wasu kuwa za su wuce masauki ne kawai su samu su huta kasancewar sun gabatar da nasu tun ranar 10 ga watan na Dhul Hajji.