Monday, December 15
Shadow

Kalli Bidiyon yanda wasu matasa suka Hàllàqà wani shugaban Fulani a jihar Benue, Sojoji sun kama wanda ake zargi suka damkawa ‘yansanda

Rahotanni daga Ogbobia, dake jihar Benue na cewa, wasu matasa sun yiwa wani shugaban Fulani Kwantan Bauna suka hallaqashi.

Sun bai wannan aika-aika ne yayin da yake kan hanyar zuwa garken shanunsa, hakanan sun bi garken shanun suka kashe su sannan suka sace wasu.

Wani dake tare da shugaban Fulanin da ya samu kubuta daga hannun maharan ya garzaya gida ya fada, fulanin sun je suka gayawa wasu sojoji dake wajen.

Ko da sojojin suka je wajan sun tarar da muharan akan gawar shugaban fulanin.

Suna ganin sojojin sai suka tsere.

Sojojin dai sun bisu inda suka kama guda daya suka mikashi hannun ‘yansanda.

Karanta Wannan  A Karshe Dai Mutumin Da Ya Yi Tattaki Daga Jigawa Zuwa Kano Domin Ganin Gwamna Abba Kabir Ya Isa Kofar Fadar Gwamnatin Kano, Inda Ya Ce Ko Zai Yi Shekara Guda Ba Zai Tafi Ba Har Sai Ya Ga Abba

Saidai Fulanin sun ce daga baya sun samu labarin ‘yansandan sun sakeshi.

shahararren dan fafutuka, VDM ne ya bayyana hakan inda ya wallafa hotunan yanda lamarin ya faru, yace fulanin garinne da kansu suka sanar dashi.

Yayi kira ga shugaban ‘yansandan Najeriya da ya binciki lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *