
Kafar Brekete Family ta wallafa Hoton Malam Nura da ake zargi da yiwa yara 9 lùwàdì a Abuja.
Sannan an kira mahaifinsa inda yace an kara gishiri a labarin da matan ke bayarwa.
Mahaifin nasa yace da aka fara zargin dansa, da kansa ya daukoshi ya mikawa hukuma amma gashi yanzu ana masa karyar wai shi ya koyawa da nasa yin Luwadin.
Sannan ba kamar yanda aka watsa a baya ba, cewa, ‘yansanda sun saki Nura, Ordinary President ya ce sun samu rahoton cewa Nura na gidan yari.