
Matar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari ta bayyana cewa, marigayi mijin nata ya amince da cewa tana son kasheshi.
Tace an rika yada rade-radin cewa, tana son ta kashe Mijin nata a fadar shugaban kasar inda tace har ta kai ga Buharin ya fara yadda da abinda mutanen ke cewa.
Tace Buhari ya canja mata kwata-kwata ya rika kulle kofa da sauransu.
Tace rashin lafiyar da yayi na da alaka da canjin abinci da rashin samun abinci me gina jiki.
Tace amma da aka kaishi kasar waje ya samu sauki.
Tace babu gaskiya a maganar cewa, guba ce aka sawa Buharin.