
Kungiyar ‘yan kasuwar Man fetur ta IPMAN ta baiwa membobinta shawarar su fara sayen man fetur daga matatar man Dangote.
Shugaban kungiyar, Abubakar Maigandi Shettima ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda yace saye a wajan matatar man Dangote yafi musu sauki fiye da shigo da man daga kasashen waje.
Yace kuma suma suna kokarin su gina tasu matatar man fetur din.
Hakan na zuwane bayan da Dangote ya karya farashin man fetur din zuwa Naira 740 akan kowace lita kamar yanda wasu gidajen man fetur na MRS ke sayarwa.