
Kafar Channels TV suna shan suka saboda yanda suka rubuta Rahoton abinda ya faru a masallaci a jihar Borno jiya.
Abin fashewa ya fashe a masalacin jihar Borno inda wasu suka rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata.
Saidai Channels TV a rahoton data kawo tace abin fashewar ya fashene a Maiduguri yayin da ake bikin Kirsimeti.
Da yawa dai sun zargi Channels TV da Munafurci saboda bas saka cewa a masallaci abinnya faru ba hakanan wasu na cewa babu abinda ya hada tashin abin fashewar da Kirsimeti tunda ba a coci ya faru ba.