
Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashim Dungurawa ya roki gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso cewa kada su fita daga jam’iyyar su koma APC.
Yayi wannan roko ne yayin da rahotanni suka fito cewa Abba zai koma APC ba tare da kwankwaso ba.
Hashim Yace kada su koma jam’iyyar da suka yi adawa da ita a baya.