
Malam Dr. Jamilu Aliyu ya bayyana cewa yana tare da Sheikh Salihu zaria game da kin biyan Haraji da gwamnati ke kokarin sakawa Talakawa
Saidai yace baya tare da Malam Salihu Zaria akan cewa wai a Dumama ‘yan Majalisa, yace ba koyarwa lr Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) bace dumama shuwagabanni.
Yace Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi umarni da a yi hakuri idan aka samu shuwagabanni marasa adalci.
Malam kuma yace wasa yayi yawa a wa’azin Sheikh Salihu Zaria inda yace ya kamata ya gyara.