Monday, December 16
Shadow

Sakonnin barka da safiya masu dadi

SAKON BARKA DA SAFIYA

Amincin Allah da yardarsa su tabbata a gareki.
Hakika kowacce safiya tana zuwa da irin nata yanayi. Ina fatan zaki kalli mudubi a lokacin da kike karanta wannan sakon,

domin kiga irin baiwar kyau da Allah ya kara miki a cikin wannan sassanyar safiyar.

Ina fatan sakona ya zamo Abu mafi farin ciki da ya fara riskarki a cikin wannan rana .
Barka Da safiya.

Ke ce kawai yarinya a duniya a gare ni, kuma duk ranar da duniya ta juya ta fuskanci rana, ina farin ciki da na tashi tare da ke. Barka da safiya, kyakkyawan fure na!

Aslm

**Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin dukkan halittu.
**wanda ya halicci kowace xuciya tare da soyayyar mai kyautata mata.
**hakika kece kika kasance mai kula da xuciyata sannan mai sanyata farinciki a ko da yaushe.
**kin kasance kina kula da ni fiye da yaddama nake kula da kaina..
**a baya ina daukar soyayya a matsayin shirme da bata lokaci. Amma bayan nayi gamo dake na tabbatar da cewa tsantsar farinciki da nishadi da walwala yana acikin soyayyar gsky.
**nariga nayi nisan acikin sonki tayadda bana iya ganin duk muni ko sharri naki sai dai kyawu da kuma alkairi.
**hakika kin wadata xuciyata da ingantaccen farin ciki mara misaltuwa.
**A karshe ina rokon Allah yabani dama da ikon kyautata maki da kula dake a kowana lokaci.

Karanta Wannan  Kalaman love

SAKON BARKA DA SAFIYA.

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *