Tuesday, January 13
Shadow

Na yi mamaki da naji Kwankwaso ya bayyana ni a matsayin makiyinsa>>Inji Ganduje

Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, yayi mamaki da ya ji Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyanashi a matsayin makiyinsa.

Yace, shi baya kallon Kwankwaso a matsayin makiyi.

Yace ya kamata ace sun wuce wannan wurin, Yace a yanzu hadin kai a Kano na da matukar Muhimmanci.

Yace yana kiran Kwankwaso ya hakura da siyasa ya sanyawa zuciyarsa ruwan sanyi.

Ganduje ya kuma yiwa Abba maraba da zuwa jam’iyyar APC.

Karanta Wannan  Buhari Munafiki ne kuma bai amfani Najeriya da komai ba sai tarin bashin da ya sauka ya bari>>Inji na kusa da Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *