
Rahotanni sun bayyana cewa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya amincewa Abba Kabir Yusuf ya koma jam’iyyar APC.
Saidai a wata sabuwar sanarwa daga Jam’iyyar NNPP ta karyata wannan Rahotan wanda kafar Premium times ta ruwaito.
Sakataren jam’iyyar ta NNPP, Ladipo Johnson ya bayyana cewa, cewa wannan rahotan ba gaskiya bane.
Yace wanda zasu koma jam’iyyar APC su koma amma su daina yaudarar Talakawa da cewa, wai Kwankwaso ya amince musu.