An Gudanar Da Addu’ar Cikar Mahaifiyar Shugaba Tinubu Shekaru Sha Daya Da Rasuwa
…wanda shugaban hukumar kula da almajirai ta kasa ya jagoranta a yau Juma’a
Daga Mustapha Narasulu Nguru
Shugaban hukumar kula da almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta na kasa, Dr. Muh’d Sani Idriss Phd ya jagoranci addu’a ga mahaifiyar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu GCFR, wanda aka gabatar yau Juma’a.
Shugaban hukumar ya yi addu’a a gare ta sosai a yau Juma’a 21/06/2024 a yayin da take cika shekaru sha daya da barin duniya.
Cikin jawabansa ya rokar mata rahama ga Allah (SWT) kamar yadda addini ya tanadar.
Muna fatan Allah Ya yi mata rahama da sauran y’an uwa musumal. Allah Ya sa Aljannah makoma.