KUTURU DA KUDINSA…
Mene Ne Aibu Don Barirah Ta Saka Takalmin Kimanin Naira Dubu Dari Biyu A Wankan Sallah?
Takalmin da Barirah Musbahu ta saka bai kamata ya zama abin cece ku ce ba a kafofin sada zumunta ba.
Duk wanda ya san Barirah Musbahu ya san ta shahara ne wajen shiga gasar “GIVEAWAY” a kafofin sada zumunta, yanzu kuma ta zama cikakkiyar yar crypto (kasuwancin yanar gizo ta zamani).
Hakika idan ka san irin makudan Kuɗaɗen da ake samu a hakar crypto bai kamata ka fara tuhumar ta ina ta samu kuɗin sayan wannan takalmin mai tsada a matsayin ta na matashiyar budurwa.
Kuma duk wanda ya riki harkar crypto hannun bibbiyu to zaisa abinda yafi haka ma tsada saboda irin kuɗaɗen da ake samu a crypto kuma na halal ga wanda ya kiyaye haram.
Barirah Musbahu ba’a iya crypto ta tsaya ba ‘yar kasuwa ce mai siya da siyarwa ta samu ribanta, dan haka ayi crypto kuma a haɗa da nasa’a domin tafi daɗi da kuma samun kuɗi lokaci guda.
Daga Hafiz Ali