Friday, January 23
Shadow

DSS sun hanani ganawa da iyali na da Lauyana>>Inji Abubakar Malami

Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami ya koka da cewa, Hukumar DSS sun ki barinshi ya gana da iyalansa da lauyansa.

Ya bayyana hakane ta bakin lauyansa, Muhammad Doka inda yace tunda DSS suka sake kama Malami bayan an bayar da belinsa, sun hanashi ganawa da kowa.

Yace zargin gano Makamai a gidan malami da kuma cewa, wai ana zarginshi da hannu a ayyukan ta’addancy duk karyane.

DSS dai sun sake kama malami, jim kadan bayan da aka sakeshi daga gidan Gyara hali na Kuje.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Bangaren Aminu Saira sun yi karin hasken kan haska shirin Labarina duk da rasuwar Fulani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *