
Rayukan ‘yan Najeriya ya baci sosai ana ta cece-kuce bayan ganin dan gidan Ministan babban birnin tarayya Abuja, Joaquin Wike sanye da takalmin da aka yi kiyasin kudinsa sun kai Dala $2,370, watau kwatankwacin sama da Naira N3,705, 000.
Ya saka takalmin ne a wajan bikin kammala karatun da yayi daga Kings College dake Birnin Landan na kasar Ingila.
Da yawa dai na tambayar inda dalibi wanda yanzu ne ya kammala karatu baya aikin komai dan shekaru 25 ya samu kudin sayen takalmin Naira Miliyan 3?