Hakika Maķàsañ Al’ummar Arewa Suna Tare Da Su
Daga Bashir Babandi Gumel
Jami’an tsaro sun kama wannan matar da daruruwan albarusan bindiga za ta kai yankin Yantumaki dake cikin karamar hukumar Dan’musa a Jihar Katsina kamar yadda ta bayyana yayin da Jami’an tsaron suke yi mata tambayoyi.
Wannan kamu yana zuwa ne kwana daya da kaiwa wani mummunan harin ta’addanci a garin Maidabino dake karamar hukumar ta Danmusa wanda ya yi sanadiyar kashe mutane 9 da kona motoci, gidaje, da satar kayakin masarufi da mutane sama da hamsin wadanda aka tafi dasu daji da sunan garkuwa dasu.
Allah ka kawo mana karshen munafuka da masu yin zagon kasa ga harkokin tsaro da ke cikinmu tare da wannan masifa ta matsalolin tsaro da muke fama da su a yankin Arewa da kasa baki daya.