
Rahotanni sun bayyana cewa, An bude masallaci mafi girma a kasar Amurka a garin Dearborn Heights, dake Michigan.
An bude masallacinne a yayin sallah karama inda aka yi Sallar Idi ta farko a ciki.
Rahotanni sun ce har yanzu akwai sassa daban-daban na masallacin da ba’a gama ba kuma idan aka kammala za’a rika karantarwa a ciki sannan za’a rika yin shirye-shiryen tallafawa matasa.