
Ni ‘yar Najeriya ce, Mijina dake zaune a kasar Ingila ya kawoni Kasar Ingila in zauna a karkashinsa a matsayin dependent.
Amma yanzu ya cireni, ya daina daukar nauyina, shine nake neman ku taimakamin a samu wani ya dauki nauyina.
Hukumar kasar Ingila sun bani kwanaki 60 in samu wani ya dauki nauyina ko su koroni Najeriya, ni kuma banson dawowa Najeriya, Dan Allah ku taimakamin.
Saidai wani da ya santa yace.
Wasu ne suka zugata, wai ta nemi mijinta ya saketa, idan ya saketa zata samu tallafi daga gwamnati idan ta hada da kudin aikinta, zasu isheta ta rike kanta.
Haka kuwa aka yi ta gayawa mijinta ta gaji da aure ya saketa, shi kuma bai yi watawata ba ya saketa sannan ya cireta daga daukar nauyinta da yake
Shine Kasar ta Ingila ta bata kwanaki 60 ta samu wani ya dauki nauyinta ko a mayar da ita gida Najeriya