Monday, December 16
Shadow

YANZU-YANZU: Tinubu Ya Aika Da Ƙudirin Biyan Mafi Karancin Albashi na Dubu N70,000 Ga NASS

A ranar Talata ne shugabań kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da kudirin dokar mafi karancin albashi ga majalisar wakilai dòmin tantancewa tare da amincewa da shi.

Ań karanta wasikar Tinubu a zaureń majalisar, inda ta tanadi sabon mafi karanciń albashi na kasa da kuma tsarin doka na aiwatar da albashiń da aka amince da shi.

A cikin wasikar, shugabań ya bukaci ‘yań majalisar da su gaggauta amincewa da kudurin dokar mafi karancin albashi dòmin tabbatar da aiwatar da shi cikin gaggawa domin amfanin ma’aikatan Najeriya.

Tinubu ya kuma nemi gyara ga dokar ‘yan sandan Najeriya kamar yadda sashe na 58 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa gyara ya ta nada.

Karanta Wannan  RANAR HAUSA: Dole Mu Tuna Da Marigayi Sheik Abubakar Mahmoud Gumi A Wannan Rana

Hakan na zuwa ne lokacin da Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa.

Hakan ya biyo bayan jerin tarurrukan da wakilan gwamnatin Najeriya suka yi da kungiyoyin kwadago.

Sai dai ana sa ran ‘yan majalisar za su halasta mafi karancin albashi na N70,000.

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *