Thursday, December 26
Shadow

Menene amfanin gemun masara

Gemun masara abune da ake samu a danyar masara me launin gwal wanda mafi yawanci yaddashi ake.

Amma yana da matukar amfani ga lafiyar dan adam. Wasu daga cikin amfanin gemun masara sun hada da.

Maganin hawan jini, yana sanya hawan jini ya sauka sosai saidai masana sun yi gargadin cewa, kada a shashi da yawa ko kuma a rika shanshi tare da maganin hawan jini saboda zai iya sanya jinin ya sauka fiye da yanda ake bukata.

Yana kuma maganin ciwon suga, yana sanya suga ya sauka sosai, saidai masana kiwon lafiya sun yi gargadin kada a rika shanshi tare da maganin ciwon suga dan zai iya sanya suga ya sauka fiye da yanda ake bukata.

Karanta Wannan  Amfanin tuwon masara

Yana kuma yin anti-age, watau maganin abubuwan dake kawo saurin tsufa a jiki.

Ana kuma amfani dashi wajan rage kiba da maganin ciwon kirji.

Saidai mata masu ciki su kiyaye kada su rika ci ko amfani da gemun masara saboda yana iya haifar da bari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *