Tabbas masana sun bayyajan cewa Wiwi na taimakawa wajan gyaran gashi.
Saidai Yin amfani da ita ta yanda bai kamata kuma yana sawa gashi ya zube.
Saidai amfani da wiwi a wajan gyaran gashi ba wai yana nufin a shata kamar tababa ko a taunata ba.
Yana nufin a rika shafata akan gashi dan gashin ya kara girma da tsawo da hana bushewa da karyewa.
Masana aun bayar da shawarar cewa ana iya hada man kwakwa ko man zaitun da wiwi a rika shafawa a akai a tabbatar ko ina ya samu.
Sannan idan ana son a ga sakamako me kyau, sai an rika shafawa a kullun.
Ko kuma idan ba za’a iya shafawa kullun ba, ana iya shafawa sau daya a sati.