Ana Amfani da Tumfafiya wajan maganin makero.
Ga wanda basu sani ba, Sunan Tumfafiya da Turanci shine Apple of sodom ko Calotropis Procera, ana kuma ce mata Giant Milkweed.
Yanda ake yi shine za’a wanke wajan da makeron yake akai sannan a zuba ruwan Tumfafiya a wajan a shafa. Haka za’a rika yi har sai ya warke.
Hakanan Tumfafiya na da alaka da tafowar gashi saboda a wani kaulin tana maganin sanko ga maza.
An yi amannar ruwan tumfafiya yana taimakawa samun tsawon gashi.
Yanda ake amfani dashi shine ana shafawa akai ne a tabbatar ta tabo har matsirar gashin. A bari na dan mintuna kamina wanke.
Hakanan ruwan na tumfaniya na maganin amosanin kai ko dandruff. Shima ana matsoshine a rika shafawa akan, insha Allahu za’a warke.
Ruwan na Tumfafiya yana kara tsawon gashi da kuma hanashi faduwa.
Hakanan Ruwan Tumfafiya na taimakawa wajan magance abubuwan dake kawo tsufar fata da wuri watau Oxidative. Ana iya amfani dashi kadai ko kuma a hadashi da Dead Sea Water.
Saidai a kiyaye, Ruwan Tumfafiya na da guba, a wanke hannu sarai da duk wasu sauran abubuwan da aka yi amfani dasu bayan an kammala aiki dashi.