Saturday, December 21
Shadow

‘Ya kamata a ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a Najeriya’

Cibiyar tattarawa da yaɗa bayanai kan rikice-rikice (CCC) ta yi gargaɗin cewa garkuwa da mutane na ƙaruwa a Najeriya, inda ta yi kira ga Gwamnatin Tarayyarv ƙasar da ta ayyana dokar ta-ɓaci domin magance matsalar.

Shugaban CCC, Manjo Janar Chris Olukolade, mai ritaya, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa matsalolin za su iya ta’azzara idan ba a yi abin da ya dace ba, wanda hakan zai ƙara jefa rayuwar al’umma cikin matsala da ƙara taɓarɓarar da matsalar tsaro.

Sanarwar ta ƙara da cewa garkuwa da mutane ta rikiɗe zuwa wata babbar harka ta kasuwanci, inda ƙungiyoyin ta’addanci ke amfani da lamarin domin samun kuɗin shiga.

Karanta Wannan  NAFDAC ta yi gargadin daina Amfani da wani turaren Nivea Roll-On saboda illarsa

“Sace mutum da aka yi na kwana-nan shi ne sace basarake a Masarautar Sokoto, da sace ɗaliban jami’a masu karatun kiwon lafiya guda 20, waɗanda aka sako daga baya, da kuma cigaba da riƙe Dokta Ganiat Popoola.”

CCC ta bayar da shawarar a tunkari matsalar da ƙarfi ta hanyar amfani da fasahar zamani da bibiyar harkokin jami’an tsaro da kuma magance matsalolin rayuwa da mutane suke fuskanta.

Haka kuma cibiyar ta yi kira ga ƙasashen waje da su taimaka wa Najeriya wajen yaƙi da matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *