Wani ma’aikacin filin jirgin sama a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano me suna Auwalu Ahmed Dankade ya tsinci dala $10,000 kwatankwacin Naira Miliyan 15 amma ya mayar da ita ga maishi.
Auwalu Ahmed Dankade yanawa wani kamfanin kula da karbar sako aiki ne a filin jirgin saman kjma a hirarsa da Daily Trust ya bayyana cewa iyayensa sun masa tarbiyyar kada ya dauki duk wani abu da ba nashi ba, ya wadata da abinda Allah ya bashi.
Kamfanin da yakewa aiki dake Legas,ya gayyaceshi zuwa Legas din inda ake tsammanin za’a girmamashi ne.