Hukumomi a jihar Anambra sun kama wata mata da ‘ya’yanta 2 saboda lakadawa mijinta duka da suka yi.
Wadanda aka kama din sune Esther Obidigwe, Ozioma Obidigwe, da Obuka Obidigwe.
Mutumin me suna Mr Obidigwe dan kimanin shwkaru 75 ne wanda kuma tsohon ma’aikacin gwamnatine.
Yace iyalan nasa sun dade suna hada kai suna dukansa, sai da makwabta suka sa baki sannan ya samu sauki.
Yace dukan kwanannan an yi masa shine saboda diyarsa ta sayar da icce ba tare da saninsa ba.
Matar tasa dai ta amsa laifinta inda diyar ma ta amsa laifinta inda tace muguntar da mahaifinta ke son yi matace ta juya kansa.
An kamasu ne karkashin ma’aikatar kula da walwalar mata ta jihar inda kuma aka mikasu hannun jami’an tsaro.